Amurka za ta samar da karin tallafin dala miliyan 375 ga ayyukan soji a Ukraine
2024-09-25 14:28:27 CMG Hausa
Jami'ai a Amurka sun bayyana cewa, kasar za ta samar da karin tallafin ayyukan soji na dala miliyan 375 ga Ukraine, ciki har da makamai masu linzami na “Javelin” da sauran kayayyakin aikin soji.
Baya ga haka, wa'adin kusan dala biliyan 6 na tallafin Amurka ga Ukraine, zai kare a karshen wannan watan, kuma majalisun dokokin kasar na muhawarar ko za a sabuntawa ma’aikatar tsaro ta kasar, izinin ci gaba da samar da makamai ga Ukraine.
Rahotanni sun bayyana cewa, tun bayan barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine a watan Fabrerun 2022, Amurka ta samar da tallafin ayyukan soji ga Ukraine, wanda darajarsa ta kai sama da dala biliyan 56.2. (Fa'iza Mustapha)