NBS: mizanin rashin aikin yi a Najeriya ya kai kashi 5.4 a shekara ta 2023
2024-09-25 09:01:01 CMG Hausa
Hukumar kididdiga ta kasa a tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, mizanin rashin aikin yi a Najeriya ya kai kashi 5.4 a shekarar bara ta 2023.
Daraktan harkokin sadarwa da hulda da jama’a na hukumar Mr. Sunday Ichedi ne ya bayyana hakan cikin wani rahoto na awon mizanin da hukumar ta fitar ranar Talata 24 ga wata a birnin Abuja.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Rahoton ya zayyano wasu daga cikin jihohin da rashin aikin yi ya fi yin katutu, inda jihar Abia ke da adadin kaso 18.7 yayin da jihar Nasarawa ke da kaso 0.5 na marasa aikin yi wanda ita ce jiha dake da karancin marasa aikin yi a Najeriya.
Mr. Sunday ya bayyana rahoton na 2023 a matsayin irinsa na farko wanda aka fitar bisa bin ka’idojin da kungiyar kodago ta duniya ta fitar a zango na 4 na shekara ta 2022 da kuma zango na 3 na shekara ta 2023.
Binciken ya nuna cewa rashin aikin yi ya fi yawa a tsakanin masu ilimin gaba da sakandire wanda yake da kaso 9.4 a kididdigar 2023, sai kaso 6.7 ga wadanda suke da shedar karatun sakandire, masu ilimin firamare kuma sun kai kaso 4.4 sai kuma kaso 3.2 ga mutanen da iliminsu ya tsaya kawai ga karatun manya wato yaki da jahilci. (Garba Abdullahi Bagwai)