NAFDAC ta kwace magungunan da ambaliyar ruwa ya shafa na sama da naira Buliyan 5 a Maiduguri
2024-09-25 09:05:24 CMG Hausa
Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna a tarayyar Najeriya ta gudanar da wani samame a wasu kasuwannin dake birnin Maiduguri inda ta samu nasarar kwace magungunan da ruwa ya lalata daga wajen ’yan kasuwa.
Cikin wata sanarwar da aka fitar jiya Talata 24 ga wata wadda take dauke da sa hannun daraktan hukumar mai lura da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Mrs Kenneth Azikiwe ta yi bayanin cewa, jami’an hukumar sun kai samamen ne a kasuwannin magunguna da abinci dake Gamboru da Gwange da kuma Monday Market.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Daraktar ta yi bayanin cewa, makasudin wannan samame dai shi ne domin tabbatar da ganin an dakile yaduwar magunguna da abinci da suka gurbace sakamakon taba su da ruwan ya yi, yin hakan kamar yadda ta fada zai taimaka wajen kare jama’a daga barazanar kamuwa da cututtuka.
Bayan afkuwar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri wanda ya cinye kasuwar magunguna ta Gomboru, hukumar ta hanzarta bayan da umarnin rufe kasuwar bayan da wasu ke sake busar da irin wadannan magunguna suna sayarwa jama’a. (Garba Abdullahi Bagwai)