logo

HAUSA

An yi ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen kasar Sin da Jamus

2024-09-25 14:19:54 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwararsa ta kasar Jamus Annalena Baerbock jiya Talata, a birnin New York na Amurka.

Yayin ganawar tasu, Wang ya bayyana cewa, Sin na fatan kara zurfafa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakanin kasashen biyu. Yana mai fatan Jamus da EU za su nace ga matsayin bude kofa da yin shawarwari, da ma kiyaye ka’idojin ciniki tsakanin kasa da kasa da halastacen yanayin takara mai adalci cikin hadin gwiwa.

A nata bangaren, Baerbock ta ce, Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi muhimmanci ta Jamus, kuma kasarta na nacewa ga manufar kasar Sin daya tak a duniya ba tare da canjawa ba. Ta ce Jamus na fatan kara hadin kai da Sin don samun sulhu karkashin mabambantan hukumomin kasa da kasa, ciki har da MDD, da ma nuna himma da gwazo wajen gagguta bunkasuwar huldar EU da Sin. (Amina Xu)