logo

HAUSA

An gudanar da taro mai taken "A rubuce a sama: Labarina na kasar Sin" don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a Mexico

2024-09-24 14:06:03 CMG Hausa

 

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya kaddamar da taro mai taken "A rubuce a sama: Labarina na kasar Sin" a birnin Mexico na kasar Mexico a ranar 20 ga watan nan da muke ciki bisa agogon wurin, don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. 

Yayin kaddamar da bikin, shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Haka kuma, jakadan Sin dake kasar Zhang Run da shugabar kwamiti mai kula da harkokin Asiya da tekun Pasifik na majalisar dattawa ta kasar Mexico kana tsohuwar shugabar rukunin sada zumunta tsakanin Sin da Mexico na majalisar wakilan kasar Madam Yeidckol Polevnsky, da sauran wakilan kasar fiye da 100 daga bangaren siyaysa da kafofin watsa labarai da kuma malamai da daliban jami’ar kasar mai zaman kanta da na kwalejin Mexico, sun halarci taron.

Mahalarta taron sun kai ga matsaya daya cewa, fahimtar bunkasuwar kasar Sin, ba kawai zai taimaka musu wajen fahimtar yadda kasar ke kokarin zamanintar da kanta ba, har ma zai taimaka wajen karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu  da ma sauran kasashen Latin Amurka, da ma tabbatar da bunkasuwarsu ta bai daya.(Amina Xu)