logo

HAUSA

Wakilin musamman na Xi Jinping ya halarci taron tattauna kan makomar duniya

2024-09-24 14:19:58 CMG Hausa

 

Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin, a matsayin wakilin musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya halarci taron tattauna kan makomar duniya da ake gudana a birnin New York, inda ya yi jawabi mai taken “Kafa makoma ta bai daya cikin hadin kai da samar da makoma mai haske”.

A cikin jawabinsa, Wang Yi ya ce, ana da duniya daya tak, dole ne kasashen duniya sun yi hadin gwiwarsu don kiyaye ta. Shawarar kafa kaykkaywar makomar Bil Adama ta bai daya da raya shawarar “ziri daya da hanya daya” mai inganci da kuma shawarar raya duniya da ta tabbatar da tsaron duniya da Xi ya gabatar, sun samar da sabon tsari ga Bil Adama wajen tinkarar kalubalolin dake gabansu cikin hadin gwiwa, da samar da sabuwar taswirar raya duniya mai kyau.

Wang Yi kuma ya jadadda ra’ayoyi guda 4 da Sin take dauka, wato kafa makoma mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kafa makoma mai wadata da samun bunkasuwa, da kuma kafa makoma bisa adalci da daidaici kana da kafa makoma mafi kyau.

Ban da wannan kuma, Wang ya nanata niyyar Sin ta hadin gwiwarta da sauran kasashe, don hanzarta kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da samar makomar duniya mai kyau. (Amina Xu)