Kasar Sin Na Shirin Zuba Karin Jari Ga Bankunan Kasuwanci Guda 6
2024-09-24 14:43:35 CMG Hausa
A gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin da aka yi a yau Talata, shugaban kwamitin sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin hada-hadar kudi na kasar Sin Li Yunze ya bayyana cewa, Sin tana shirin zuba karin jari ga manyan bankunan kasuwanci guda 6 bisa nazarin da aka yi, don inganta karfinsu na gudanar da harkokin hada-hadar kudi ba tare da tangarda ba, da ma kara musu kwarin gwiwar taka rawa wajen raya sana’o’i masu samar da kayayyaki. An ce, za a samar da wadannan kudade ne a mataki-mataki tare da yin la’akari da halin da kowannensu ke ciki. (Amina Xu)