Sakatare janar na MDD ya kadu da ta’azzarar lamura tsakanin Lebanon da Isra’ila
2024-09-24 14:10:13 CMG Hausa
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ya kadu da ta’azzarar yanayi a yankin da ba a yaki da ya raba Isra’ila da Lebnanon, da tarin fararen hula da lamarin ya rutsa da su, ciki har da yara da mata, kamar yadda hukumomi a Lebanon suka bayyana.
Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ruwaito Antonio Guterres na nanata bukatar dakatar da rikicin nan take, yana mai kira da a mayar da hankali kan neman mafita ta hanyar diplomasiyya, tare da kira ga dukkan bangarorin su kare fararen hula da kadarorinsu, tare da tabbatar ba a sanya su cikin hadari ba.
A cewar ma’aikatar kula da lafiya ta Lebanon, luguden wutan da Isra’ila ta kai kasar a ranar Litinin, ya kai ga mutuwar mutane 356, ciki har da yara 24 da mata 42, yayin da wasu 1,246 suka jikkata. (Fa’iza Mustapha)