logo

HAUSA

Jirgin sama samfurin Y-20 kirar kasar Sin ya nuna bajimta a wajen bikin baje-kolin jiragen sama da tsaro na Afirka

2024-09-24 16:11:42 CMG Hausa

Babban jirgin saman dakon kaya samfurin Y-20 kirar kasar Sin, ya nuna bajimta sosai, a wajen bikin baje-kolin jiragen sama da tsaro na kasashen Afirka karo na 12, wato AAD a takaice, a birnin Pretoria dake kasar Afirka ta Kudu, wanda ya zama bikin baje-kolin jiragen sama mafi girma dake jawo hankali a nahiyar Afirka.