Kasar Sin za ta bi ka’idojin WTO wajen tinkarar kalubalantarta da EU ke yi na binciken tallafin kayayyakin madara
2024-09-24 13:48:15 CMG Hausa
Ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a ranar Litinin cewa, ta samu bukatar tuntuba da kungiyar tarayyar Turai EU ta gabatar ta hannun kungiyar cinikayya ta duniya WTO, game da binciken kasar Sin na nuna adawa da ba tallafi kan kayayyakin madara na EU da aka shigo da su.
A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma’aikatar ta ce kasar Sin ta nuna bakin ciki kan yadda kungiyar EU ta kalubalanci lamarin ta hanyar tsarin warware takaddamar WTO, amma kasar za ta tinkari kalubalen bisa ka'idojin WTO.
An bayyana cewa, kasar Sin ta kaddamar da binciken adawa da ba tallafi kan kayayyakin madara na kungiyar EU ne bisa ga dokokin kasar Sin, kana a matsayin martani ga bukatar masana'antun cikin gida, kuma gwamnatin kasar Sin tana da ikon kiyaye hakkoki da moriyar masana'antunta na cikin gida. (Mohammed Yahaya)