Manufar “Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko” Za Ta Samar Da Ci Gaban Da Duniya Ke Muradi
2024-09-24 22:27:40 CMG Hausa
Wata kididdiga da aka fitar yau Talata, ta nuna cewa, adadin kamfanonin dake bangaren sarrafawa da kere-keren kayayyaki a kasar Sin ya kai miliyan 6.03, karuwar kaso 5.53 daga karshen shekarar da ta gabata.
A farkon bara ce kasar Sin ta kaddamar da manufar “sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko” da nufin zama mai dogaro da kanta a bangaren kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da samar da hajoji masu inganci tare da daukaka ayyukan masana’antu.
Kasar Sin ba ta fada, ta gaza cikawa. A kullum na kan yi mamakin yadda idan Sin ta furta abu, to sai ta kai ga cimma shi. Kuma na fahimci cewa hakan ba ya rasa nasaba da kyawawan kudurorin gwamnati, ta hanyar daukar ingantattun matakai da goyon bayan da al’umma ke ba ta da kuma kishin kasa dake akwai a zukatan dukkan bangarorin.
Har kullum, gwamnati da al’ummar kasar Sin ba sa duba moriyarsu ta kashin kai, sai yadda kasar baki daya za ta amfana. Shi ya sa idan gwamnatin kasar Sin ta gabatar da wata manufa ko burin da take son cimmawa, to al’ummarta za su yi na’am su karba da hannu bibbiyu domin bayar da gudunmuwarsu wajen cimma wannan buri.
Karuwar adadin kamfanonin da aka samu a bana, ya kara tabbatar da cewa, burin kasar Sin na zama mai dogaro da kanta na gab da cika. Wannan labari ne mai dadi ba ga kasar Sin kadai ba, har ma da sauran kasashe abokan huldarta, musammam masu tasowa, domin ci gaban kasar Sin, ci gaban su ne da duk sauran sassan duniya. Kana hakan zai kyautata wadatar kayayyakin da ake bukata da za su kasance masu inganci da rahusa ba tare da fuskantar tangarda ko kariyar cinikayya ba.
Yayin da wasu kasashe suka nace ga kariyar cinikayya, wannan manufa ta kasar Sin, za ta habaka tsarin harkokin cinikayya a duniya, haka kuma za ta bunkasa tsarin samar da kayayyaki ta yadda abubuwan da ake bukata a duniya za su wadatu. Haka kuma, kasar Sin za ta zama jagora wajen ganin dunkulewar duniya da inganta dangantakar cinikayya tsakanin sassa daban daban, wanda zai kara kawo cudanyar mabanbantan al’ummu da fahimtar juna da wanzuwar zaman lafiya da samar da al’umma mai makoma ta bai daya, wato dai, ci gaban da ake fata.
Bugu da kari, zai kara bayyana illolin kariyar cinikayya da wasu kasashe ke aiwatarwa, domin yunkurinsu na mayar da Sin saniyar ware ba zai yi nasara ba, sai dai su ware kansu daga ci gaban da duniya za ta samu ta kuma mora.