An gudanar da bikin murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin a Australiya
2024-09-24 13:45:33 CMG Hausa
Babban rukunnin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya kaddamar da bikin bayyana labaran Sin a birnin Canberra na kasar Australiya a jiya Litinin, don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin,
Yayin kaddamar da bikin, shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Kana jakadan Sin dake kasar Xiao Qian da babban darekta mai kula da aikin zirga-zirgar jiragen sama zuwa ketare da kasuwar yawon bude ido a bangaren gabashin duniya na ma’aikatar yawon bude ido na kasar Australiya Andrew Hogg da sauran jami’an kasar, sun halarci taron. Haka zalika, wakilai kimanin dari daga bangaren siyasa da masana da kafofin yada labarai da Sinawa dake kasar, su ma sun halarci taron.
Mahalarta taron sun kai ga matsaya daya cewa, Sin ta samu gagarumin ci gaba a cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, kuma tana kan wani muhimmin matsayi a duniya wajen daidaita harkokin kasa da kasa, kuma ci gaban da Sin ta samu na samar da damammaki da kuzari masu kyau ga kasashen duniya ciki har da kasashen yankin Asiya da Pacifc. (Amina Xu)