logo

HAUSA

Peng Liyuan ta halarci bikin kawance da na wasanni na matasan Sin da Amurka

2024-09-24 21:45:16 CMG Hausa

Da yammacin yau Talata ne mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta halarci bikin matasa na Sin da Amurka, mai lakabin tafiyar matasa, da taron raya al’adun matasan sassan biyu, da dandalin raya wasanni tsakanin sassan biyu, wanda ya gudana a makarantar midil mai lamba 8 dake birnin Beijing, inda kuma ta yi cudanya da wakilan matasan da suka zo daga birnin Washington na Amurka domin halartar bikin.

A watan Nuwamban shekarar 2023, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da shirin gayyatar matasa Amurkawa 50,000 karkashin shirin musaya, da samun ilimi a kasar Sin cikin shekaru 5, lokacin da ya kai ziyara birnin San Francisco na Amurka. A wannan lokaci kuma, bikin da gayyato malamai da dalibai kusan 100 daga makarantun midil sama da 10 na jihar Washington. (Saminu Alhassan)