Ziyarar Kande Gao da tawagarta a kasashen yammacin Afirka uku
2024-09-24 15:17:25 CMG Hausa
Kande Gao, mataimakiyar shugaba ce ta sashin Hausa na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, wadda ta jagoranci wata tawaga dake kunshe da mutane hudu don ziyartar kasashen Nijar, Ghana da Najeriya, daga karshen watan Agusta zuwa farkon watan Satumba na shekarar da muke ciki, ciki har da Murtala Zhang da Tasallah Yuan.
A yayin zantawar Murtala Zhang da ita, malama Kande Gao ta yi karin haske kan ziyarar da suka yi a kasashen uku, da abubuwan da suka burge ta a yayin ziyarar, kana, ta bayyana kyakkyawan fatanta gami da mika gaisuwa ga jama’ar kasashen uku. (Murtala Zhang)