logo

HAUSA

Yao Yanmei ta nuna himma da hikima don rubuta almara ta farfado da karkara

2024-09-23 21:37:52 CMG Hausa

A filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Beijing na kasar Sin, a cikin manyan fostocin da ke gungurawa a kan babban allo, ba wata shahararriyar tauraruwa mai jan hakulan mutane ake nunawa ba, ba kuma wata attajira da ta samu gagarumar nasara ba, sai dai wata mace ta gari daga dangin manoma, wadda ta nuna himma da hikima don rubuta almara ta farfado da karkara. Ita ce Yao Yanmei mai shekaru 33, shugabar kamfanin kimiyya da fasaha kan sha’anin noma na Jinghe.

A farkon lokacin zafi, ana iya ganin wasu manyan zane-zane masu kyau dake shimfide a filayen shinkafa dake karkara na birnin Xinzhou na lardin Shanxi dake arewacin kasar Sin, wadanda salonsu sun yi kama da zane-zanen da aka yi ta hanyar yin amfani da fasahar yanke takarda ta kasar ta Sin. Wadannan zane-zanen da aka yi a filin shinkafa, wadanda ke mayar da gonakai a matsayin takarda, kuma ke mayar da tsiron shinkafa kamar tawada, sun nuna yadda manoma ke daukar nauyin farfado da karkara, da bayyana fatansu na jin dadin zaman rayuwa.

Masu zane-zanen sun zo ne daga wani rukuni na “masu fasaha” na yankunan karkara, kuma Yao Yanmei ce ta mayar da su “masu fasaha”.

Yao Yanmei, wadda ta girma a yankunan karkarar Xinzhou, tun tana karama, tana ganin iyayenta suna aiki tukuru da himmatuwa a gonaki, kuma tana cin masara da dawa da aka shuka a yankin, don haka, tun fil azal ta nuna kauna sosai ga gonakai.

Lokacin da ta rubuta takardar neman shiga jami’a, ta zabi yin digiri a fannin karatu na gudanar da harkokin tattalin arziki a bangaren aikin gona.

A yayin da take karatu a jami’a, Yao Yanmei ta bi malamanta don ganin wata babbar duniya a fannin aikin gona, kamar su tsintowa, yawon shakatawa a gidajen manoma, sarrafa kayan amfanin gona da dai sauransu. Aikin noma ta al’ada ta riga ta fadada zuwa sababbin iyakoki. Noma ba ta nufin yin aiki tukuru a gonaki, kuma yankunan karkara ba su alamta “rashin ci gaba”.

Da ganin haka, Yao Yanmei ta ce, “Idan gari na ma zai iya kasancewa kamar haka, zai yi kyau sosai.” Tana matukar fatan yin amfani da abin da ta koya, kuma ta kawo canji a rayuwar danginta da ma rayuwar al’ummar garinsu.

A yayin da take aji na hudu tana karatu a jami’a, ita da gungun abokan karatunta masu kishi daidai da juna sun kafa kamfani don fara kasuwanci, suna mai da hankali kan noman kayan amfanin gona masu tsabta, da ba da ilmin kimiyya a fannin yin kirkire-kirkire na gonaki.

Su matasa ne masu cike da kwarin gwiwa wajen raya sana’arsu, amma ba su da kwarewa da fasahohi sosai. Saboda ba su yi bincike yadda yakamata kan kasuwa ba, kuma kudin da suka kashe kan shukar innabi da kayan lambu sun yi yawa, amma yawan kayayyakin da suke samar wa ba su da yawa kuma marasa inganci, don haka, ba su iya samun riba ba. A sabili da haka, a cikin kasa da shekara guda, abokan hadin kanta sun bar kamfaninta, don neman sababbin ayyukan yi. Da haka, kasuwanci na farko da Yao Yanmei ta gudanar ya bi ruwa.

Daga baya, ta samu aiki a wani kamfani mai kula da sha’anin noma a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, inda ta samu cikakkiyar fahimta game da dukkan tsarin aikin amfanin gona da ma abubuwan dake da alaka da bangaren, ciki har da yadda ake gudanar da ayyukan kasuwanci ta yanar gizo, da habaka samfura da shuka kayayyakin aikin gona da dai sauransu.

Yayin da take da shekaru 28 da haihuwa, Yao Yanmei da ba ta gamsu da halin da take ciki a wancan lokaci, sai ta tsaida kudurin komawa garinsu don raya sana’a. Ta ce, “Wannan ita ce dama ta karshe da zan ba wa kaina, komai wahala, zan yi iyakacin kokarin in gwada.”

Tabbas iyayenta da suka yi noma a duk rayuwarsu, ba sa goyon bayan ta, domin yin wannan aikin yana da wahala, da gajiya kuma ba za a iya samun kudin shiga da yawa daga aikin ba. Sun fahimci hakan kwarai da gaske. Yao Yanmei ta fahimci damuwar iyayenta, amma a matsayinta na diya mafi girma a gidansu, ta saba da daukar nauyin dake bisa wuyanta.

Ta ziyarci wurare da yawa don yin bincike, ta gano cewa, duk da cewa garinsu na Jingle yanki ne na noma na gargajiya, amma fadin yankunan gonaki ba ya da girma, kuma an raba su zuwa sassa kanana a ko’ina, hakan ya sa ba za a iya samun riba sosai ba wajen dashen kayan amfanin gona ta hanyar gargajiya.

Fasahar yanke takarda ta al’adun da aka gada daga kakan kakkani ta wurin, ta zama asalin tunanin ta na raya sana’a, Yao Yanmei, wadda ke da karfin aikatawa, ba da dadewa ba ta kirkiri wani irin zane na musamman da aka yi a filin gonaki ta hanyar yanke shinkafa, wanda ke da salon zane-zanen da aka yi ta fasahar yanke takarda, Yao Yanmei ta kira irin zane da sunan “Zane-zanen filin shinkafa ta fasahar yanke takarda”.

Bayan ta shawo kan iyayenta, ta dauki rancen kudi RMB yuan dubu 100 don kafa kamfanin kimiyya da fasaha kan sha’anin noma na Jinghe.