UNHCR: Sama da mutane 342,000 ne suka rasa muhallansu a Somaliya cikin watanni 8
2024-09-23 14:05:38 CMG Hausa
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko UNHCR ta sanar a jiya Lahadi cewa, tashe-tashen hankula da rashin tsaro da sauyin yanayi sun raba mutane fiye da 342,000 da muhallansu a cikin watanni 8 na farkon shekarar 2024 a kasar Somaliya.
Sashen kula da ayyukan kariya da sa ido a karkashin hukumar ta UNHCR, ya kuma bayyana cewa, kimanin mutane 23,000 ne suka rasa muhallansu a cikin watan Agusta kadai, inda kashi 43 cikin dari ake alakanta su da tashe-tashen hankula, rashin tsaro, ambaliyar ruwa, ko fari.
A cikin sabon rahotonta na aiki da aka fitar a Mogadishu, babban birnin Somalia, UNHCR ta ce, “Abinci, matsuguni, rayuwa, ruwa, da lafiya su ne manyan bukatun sabbin iyalan da suka rasa matsugunnansu. Yayin da yankunan Bari, Bay, Juba Ta Tsakiya, Gedo, da Juba ta kasa suka ba da rahoton mafi yawan adadin mutanen da suka isa wurinsu, wanda ya kai kashi 66 cikin dari na adadin mutanen da suka rasa matsugunansu. Kana kaso 80 cikin dari na mutanen da suka rasa matsugunansu mata ne da yara, wadanda ke fuskantar barazanar kariya, a cewar UNHCR. (Yahaya)