logo

HAUSA

Tarihin Ci Gaban Sin: Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

2024-09-23 19:00:55 CMG Hausa

 

An dade ana zazzafar muhawara game da mabambantan hanyoyin zamanantar da  kasa da hanyoyin ci gaba, sai dai a karshe burin wannan yunkuri shi ne cimma Amurka. Saboda Amurka ta kasance madaidaicin ma'auni kuma abin misali ga duka wata kasa mai burin samun ci gaba. Amma a halin yanzu, ba haka lamarin yake ba, saboda alkibla ta canja. Ma iya cewa, kyauta mafi daraja da kasar Sin ta baiwa kasashen duniya, ita ce fahimtar ya kamata akwai nau’ikan salo daban daban na zamanantar da kasa, ba ma kawai zamanantarwa ba, har ma zamani karan-kansa. Wannan shi ne abin da Tarayyar Soviet ta yi kokarin nunawa a cikin dukan tarihinta, amma a karshe ta kasa. Wannan shi ne abin da yawancin masu ra'ayin dimokuradiyya a Turai suka so su tabbatar, amma ba su samu nasarar yin hakan ba. Wannan shi ne ne burin kasashe da yawa a kudancin duniya, amma ayyukan ci gabansu har yanzu galibi ba su kai mizani ba.

Tabbas, shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin ba ta kasance cikin nasarorin da aka samu da kuma abubuwan ban mamaki kawai ba. Wadannan shekarun suna cike da wahalhalu da ayyuka masu dorewa.  Nasarar da kasar Sin ta samu ba sakamakon gumi ba ne kawai, har ma da hawaye. Kwararu kan harkokin kasa da kasa suna ta musayar yawu game da lokacin da kasar Sin za ta zarce Amurka a matsayin wadda ke kan gaba a fannin tattalin arzikin duniya. Sai dai amsar wannan tambaya ta dogara ne a kan hanyoyin bincike, da alkaluma da ake da su, da sauran abubuwa da dama, wadanda galibi a kan samu son zuciya a cikin hukuncin manazarta. Duk da haka, yawancin hasashe na nuni da cewa gibin dake tsakanin Sin da Amurka a muhimman fannoni zai ci gaba da raguwa cikin lokaci. To, duk dai yadda makomarta za ta kasance, babu wanda zai musanta nasarar da kasar Sin ta samu a tarihi.  Kuma abu mafi muhimmanci game da hakan shi ne cewa tushen wannan nasara ba kawai ya ginu kan tsarin cikin gida da kuma kimanta salon ci gaban da aka shigo da shi daga kasashen waje ba, har ma da yin amfani da wata hanya ta musamman ta asali bisa la'akari da takamaiman yanayi na kasa. Ya kamata nasarar da kasar Sin ta samu ta koya mana cewa, kowace al’umma babba ko karama, mai wadata ko talaka, a arewaci ko kudancin duniya, ta zama jagorar makomarta bisa la’akari da bukatu da kuma yanayinta.  (Mohammed Yahaya)