logo

HAUSA

Taron kolin MDD ya zartas da yarjejeniyar makomar duniya

2024-09-23 11:20:20 CGTN Hausa

 

An bude taron kolin MDD kan makomar duniya na kwanaki biyu a jiya Lahadi a hedkwatar majalisar dake birnin New York. Inda aka zartas da yarjejeniyar makomar duniya da sauran bayanai masu nasaba, ta yadda za a ci gaba da raya tsarin gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori da suka dace da bunkasuwar nan gaba da kokarin kafa wata duniya mai tsaro dake da zaman lafiya da adalci da daidaito da kuma hakuri da juna da dorewa da wadata.

Shugaban babban taron MDD karo na 79 Philemon Yang ya yi jawabi a gun taron cewa, ana tsaka da karkata hanyar samun bunkasuwa, da ma fuskantar kalubalolin da ba a taba ganin irinsu ba, saboda haka ana bukatar daukar mataki cikin hadin gwiwa. Wannan yarjejeniyar ba tinkarar kalubalolin da muke fuskanta yanzu za ta yi kadai ba, har ta aza harsashi mai inganci ga kafa tsarin duniya mai dorewa da adalci da zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa, kalubalolin sun zo da damammaki, kana makomar tana hannun bil Adam.

Babban sakandaren MDD Antonio Guterres ya yi jawabi cewa, duniya na cikin wani muhimmin lokaci na tinkarar sauye-sauye da karkatar hanyar samun bunkasuwarta, dole ne an dauki mataki a zagaye na farko da ya zama wajabi, don kyautata da kara hadin kan kasa da kasa. Ya yi kira ga mahalarta taron da su yi wa taron kwaskwarima, don kafa halastaccen hukumomin duniya cikin adalci bisa tushen tsarin mulkin MDD. (Amina Xu)