logo

HAUSA

Shugaban kasar Mali ya sha alwashin dakile ayyukan ta'addanci

2024-09-23 13:37:22 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne shugaban kasar Mali Assimi Goita ya sha alwashin karfafa yaki da ta'addanci, yana mai jaddada aniyarsa na samar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaba a kasar.

Goita ya bayyana hakan ne bayan wani faretin sojoji na bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kan kasar Mali.

Ya kara da cewa, “Za mu fatattaki wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai ba dare ba rana har sai kasarmu ta kasance babu barazana kwata-kwata”. 

Yayin da yake yabawa al'ummar kasar Mali wadanda duk da kalubalen da ake fuskanta, suna ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar sojojin kasar a kokarinsu na kare al'ummar kasar, Goita ya jaddada bukatar hadin kai mai karfi da rundunar tsaron kasar, yana mai cewa, nasara a wannan yaki na bukatar goyon bayan ’yan kasa da kuma abokan hulda. (Yahaya)