Mataimakin firaministan kasar Sin ya ce kasar na shirin samun girbi mai yawa
2024-09-23 13:30:19 CMG Hausa
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong ya bayyana a ranar Lahadi cewa, kasar Sin na shirin sake samun girbin hatsi mai yawa a bana, bayan da manoma da jami’ai daga sassa daban daban na kasar suka yi aiki tukuru don shawo kan illolin da bala'u daga indillahi suka haifar, da kuma kara yawan noman hatsin na rani da yawan noman shinkafa mai saurin girma.
Liu, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a yayin rangadin da ya kai gundumar Lankao ta lardin Henan na tsakiyar kasar Sin, inda ya halarci wani babban taron kasa na murnar bikin girbi na manoman kasar Sin karo na bakwai.
Liu ya yi kira da a himmatu wajen inganta aikin farfado da yankunan karkara gaba daya, ta hanyar aiwatar da manufofi da tsare-tsare na kwamitin kolin JKS, ta yadda za a aza harsashin zamanantar da aikin gona da yankunan karkara, da kuma gina kasar Sin don ta zama cibiyar aikin gona.
A yayin bikin, Liu ya kuma halarci wani baje koli inda aka nuna irin nasarorin da aka samu ta hanyar koyo da kuma amfani da kwarewar shirin farfado da yankunan karkara, ya kuma gane ma idanunsa kayayyakin aikin gona masu inganci da kwarewar masu sana'ar hannu a yankunan karkara. (Yahaya)