logo

HAUSA

An gudanar da bikin da ya shafi makamashi na nan gaba a birnin New York

2024-09-22 16:21:11 CMG Hausa

A lokacin da ake shirin kaddamar da taron makomar dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, an gudanar da wani biki mai taken "Makamashi na nan gaba" a birnin New York na kasar Amurka, a ranar 21 ga wata.

Kasashen da suka halarci bikin sun fitar da "Sanarwar makamashi na nan gaba", da nufin inganta mu'ammala, da hadin gwiwa a fannin makamashi tsakanin mabambantan kasashe, tare da sa kaimi ga sauyawar tsare-tsaren makamashin duniya, da neman samun ci gaba mai dorewa ta fuskar harkar makamashi.

Hukumar hadin gwiwar kasashen duniya a fannin makamashi ta yanar gizo ta Internet, wadda kasar Sin ta kaddamar da aikin kafa ta, da kuma ofishin tsara dabaru na neman ci gaba mai dorewa na MDD ne suka karbi bakuncin bikin, inda sama da baki 200 daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30 suka halarci bikin.

A wajen bikin, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, yadda za a gina duniya mai tsafta da kyan gani, da tabbatar da makomar dan Adam mai kyau, wani babban batu ne da ke bukatar tunanin daukacin gamayyar kasa da kasa tare. Ya kamata al'ummomin kasa da kasa su karfafa hadin kai, da daukar matakan da suka dace wajen tinkarar kalubaloli, irinsu tsanantar sauyin yanayin duniya, da yawan aukuwar bala'o'i a kai a kai.

Kaza lika a sa kaimi ga daidaita makamashi cikin adalci, da gaggauta aiwatar da manufofin neman ci gaba mai dorewa. Jami'in na Sin ya yi bayani kan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa da kare muhalli, a cikin 'yan shekarun nan, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin ita ce kasar dake kan gaba wajen sauya tsarin raya tattalin arziki zuwa nau'in kare muhallin halittu, mai sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa a fannin daidaita makamashi, kana mai ba da gudummawa ga harkokin kula da makamashi da aikin kyautata yanayin duniya, yayin da kokarin kare muhalli ke zama tushe ga tsarin zamanantarwa na kasar Sin.

A nasa jawabin, manzon musamman na babban magatakardan MDD kan ayyukan daidaita yanayi Selwyn Hart, ya yabawa kasar Sin bisa gagarumar gudummawar da ta bayar a fannin raya tattalin arzikin duniya, tare da tabbatar da ingancin muhallin halittun duniya. Har ila yau, ya jaddada wajibcin mai da hankali kan maganar adalci yayin da ake sauya salon makamashi zuwa mai tsabta a duniya.

A cewarsa, a halin yanzu, yawancin jarin da ake zubawa a bangaren makamashi mai tsabta a kasashe masu sukuni suke, yayin da kasashe masu tasowa da dama suka kasa samun isashen jari. (Bello Wang)