logo

HAUSA

Kungiyar ba da agajin kiwon lafiya ta kasa da kasa ta bayyana fargaba barkewar cututtuka a birnin Maiduguri

2024-09-22 14:39:40 CMG Hausa

Kungiyar bayar da agajin kiwon lafiya ta kasa da kasa ta Médecins Sans Frontières ta ce akwai barazanar barkewar Kwalara da zazzabin cizon sauro a birnin Maiduguri bayan annobar ambaliyar ruwa da ya shafi yankin.

Wakilin kungiyar a Najeriya Dr. Issaley Abdel ne ya tabbatar da hakan jiya asabar 21 ga wata cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Abuja wadda take dauke da sa hannun jami`in sadarwar kungiyar Abdulkareem Yakubu.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kungiyar ta ce muddin dai ba`a dauki matakan gaggawa ba ta fuskar samar da magunguna da taimakon jin kai lamarin zai kazanta mutuka, kasancewar a yanzu haka rashin abinci mai gina jiki da karuwar cututtukan da ake samu ta ruwa yana kara yawaita cikin hanzari musamman a yankunan da ambaliyar ta shafa.

Kungiyar ta Médecins Sans Frontières ta ce ta hango cewa za a fuskanci matsalar zazzabin cizon sauro da cutar amai da gudawa a tsakanin al`umomin musamman ma kananan yara da mata masu shayarwa.

Kamar dai yadda kungiyar ta bayyana tun kafin faruwar annobar ambaliyar ruwa kananan yara da dama suna fama da matsalar zazzabin cizon sauro da gudawa, yayin da al`amari kuma ya karu bayan annobar ambaliyar , a don haka kungiyar ke bayanin cewa lamarin zai iya karuwa fiye da kima muddin dai aka gaza wajen samar da magunguna da kayan taimakon jin kai da suka shafin tsaftaccen ruwan sha, da na tsaftar muhalli da kiwon lafiya.

Koda yake kungiyar ta MSF ta tabbatar da cewa ya zuwa yanzu jami`anta sun ziyarci sansanoni daban daban da suka hada da Galtimari, Yerwa, Ali Sheriff da cibiyar bayar da horon dogaro da kai, inda suka duba bukatun mazauna wurin tare da samar masu da tsaftaccen ruwan sha da gyara masu fitilu tare kuma da rarraba masu rigunan sauro.

Ha`ila yau kuma sun bayar da magani ga wayanda basu da lafiya dake sansanonin.(Garba Abdullahi Bagwai)