Sin ta cimma nasarar kera maganadisu mafi karfi a duniya
2024-09-22 20:10:27 CMG Hausa
Masana kimiyya na kasar Sin sun cimma nasarar kera maganadisu bisa fasahar gida mai karfin tesla 42.02, wanda ke da karfin da ya kai sama da ninkin maganadisun duniya 800,000, wanda hakan ya karya matsayin bajimtar da kasar Amurka ta kafa a fannin a shekarar 2017.
Nasarar hakan wadda ta samu a Lahadin nan, karkashin binciken masana dake aiki a dakin gwaje gwajen karfin maganadisu na cibiyar nazarin ilimin asalin halittu ta Hefei, wadda ke karkashin hukumar binciken kimiyya ta kasar Sin ko CHMFL, zai ingiza binciken kimiyyar zahiri a fannin, da ma sauran fannonin cin gajiyar fasahohi masu nasaba da hakan. (Saminu Alhassan)