Kafar Al Jazeera ta zargi dakarun Isra’ila da kutse cikin ofishinta dake birnin Ramallah
2024-09-22 16:29:55 CMG Hausa
Gidan talabijin na Al Jazeera, ta zargi dakarun Isra’ila da yin kutse cikin ofishin ta dake birnin Ramallah na yamma da kogin Jordan, inda sojojin suka umarci rufe ofishin har tsawon kwanaki 45.
Kafar mallakin kasar Qatar, ta bayyana hakan ne a Lahadin nan, inda ta ce dakarun sojin Isra’ila sun kutsa ginin ofishin, inda suka mika takardar umarnin rufe kafar ga shugaban ofishin Walid al-Omari.
Kafin hakan, rundunar sojin Isra’ila IDF, ta ce ta kaddamar da sabbin hare hare ta sama kan yankunan kasar Lebanon da yammacin jiya Asabar, da nufin lalata rokokin harba makamai na kungiyar Hezbollah, da ma sauran kayayyakin yaki na kungiyar.
Da yake tabbatar da hakan, kakakin IDF Daniel Hagari, ya ce sojojin yakin Isra’ila na ci gaba da kaddamar da hare hare ta sama kan makaman yakin Hezbollah, da nufin kawar da barazanar da fararen hula Isra’ilawa ke fuskanta. (Saminu Alhassan)