logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta hallaka sama da mutane 500 a Chadi

2024-09-22 15:38:00 CMG Hausa

A kalla mutane 503 ne ambaliyar ruwa ta hallaka a kasar Chadi tun daga watan Yulin bana kawo yanzu. A cewar wani rahoton baya bayan nan da ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA ya fitar, adadin mutanen da ambaliyar ta shafa a Chadi ya kai kusan miliyan 1.7, baya ga dubban gidaje da suka lalace.

Rahoton ya ce akwai bukatar gaggauta samar da tallafin jin kai, yayin da ake gargadi ga hukumomi cewa, karuwar ruwan sama kamar da bakin kwarya, da tunbatsar kogi na iya haifar da karin ambaliya a kasar. (Saminu Alhassan)