Gwamnatin Cote d’Ivoire ta bude wani bincike kan bacewar wani dan jaridarta a Nijar
2024-09-21 17:01:40 CMG Hausa
Gwamnatin kasar Cote d’Ivoire ta sanar a bayan wani taron ministoci na ranar jiya Jumma’a 20 ga watan Satumban shekarar 2024, cewa ta bude wani bincike kan bacewar wani dan asilin kasarta a Nijar da ke aikin jarida.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Tun farkon watan satumba, a cewar kakakin gwamnatin Cote d’Ivoire, Amadou Coulibaly, dan jarida dan asilin kasar Cote d’Ivoire, Serges Mathurin Adou, da ke aiki a birnin Yamai tun yau da shekara 20 aka rasa duriyarsa.
Bisa la’akari da labaran da kakakin gwamnati ya raiwato, ana kyautata zaton cewa Adou ya bace tun bayan amsa kiran ‘yan sandan PJ, da suka kira shi kan wata kara, a cewar labarin da matarsa ta baiwa karamin jakadan kasar Cote d’Ivoire.
Karamin jakadan ya ce sun tuntubi hukumomin shari’a na kasar Nijar da suka bayyana cewa ba su da wani labari kan wannan batu, in ji kakakin, tare da bayyana cewa ma’aikatarsa ta tattauna tare ministan harkokin wajen Cote d’Ivoire da karamin jakada da ke kula da harkokin Nijar.
“Za mu ci gaba da bincike, kuma za mu tuntubi a hukumance jakadan kasar Nijar da ke Cote d’Ivoire, domin neman sanin takamaimai abin da ke faruwa”, in ji Amadou Coulibaly.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar.