An kaddamar da rumbun adana bayanai kan tunanin Xi Jinping
2024-09-21 16:49:39 CMG Hausa
A yau Asabar ne aka kaddamar da wani rumbun adana bayanan tunanin Xi Jinping kan tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin na sabon zamani.
Cibiyoyin da suka hada da madaba'ar jama’ar kasar Sin ko People's Publishing House a Turance ne suka tsara shi, kuma an kaddamar da rumbun bayanan ne a bikin baje kolin wallafe-wallafe na zamani na kasa da kasa karo na 14 na kasar Sin da aka bude a wannan rana a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
Rumbun bayanan ya tattara tare da sabunta muhimman jawabai, makalu, umarni, sharhi, wasikun taya murna da amsoshin wasiku daga Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Kazalika rumbun bayanan ya kunshi littattafai da rahotannin labarai masu alaka da tunanin Xi Jinping.
Rumbun bayanan na samar da cikakkun bayanai masu inganci don nazari kan tunanin Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin na sabon zamani. (Yahaya)