Fasahar Sin ta kara habaka sha’anin zirga-zirgar ababen hawa mara gurbata muhalli a Afrika
2024-09-21 16:34:28 CMG Hausa
Masana kimiyya sun bayyana a jiya Juma’a cewa, fasahar motoci masu amfani da makamashi mai tsabta na kasar Sin na habaka yin amfani da ababen hawa mai amfani da wutar lantarki a Afirka.
Darektan kawancen ababen hawa mara gurbata muhalli na Afirka ko Africa E-mobility Alliance a Turance, Warren Ondanje ya bayyana a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, kamfanonin kera motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin sun mayar da kansu a matsayin manyan abokan hadin gwiwa ga karin kamfanonin Afirka da suka fara kera motoci masu amfani da lantarki.
Ondanje ya bayyana hakan ne a yayin taron makon motoci masu amfani da lantarki na Afirka na shekarar 2024, inda ya ce, "kamfanonin kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen hanzarta yin amfani da motoci masu amfani da lantarki a Afirka."
Taron na kwanaki biyar ya hallara wakilai sama da 200 da suka hada da wakilai daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da manyan jami’an gwamnati da masu kirkire-kirkire daga ko’ina a nahiyar Afirka, domin karfafa hadin gwiwa da kuma ciyar da sha’anin zirga-zirga mai dorewa gaba a nahiyar.
Kazalika, mataimakin injiniya mai sai ido a ma'aikatar kula da hanyoyi da sufuri ta kasar Kenya Michael Muchiri ya bayyana cewa, motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, suna jan hankalin masu amfani da ababen hawa da nufin kiyaye muhalli na kasar Kenya saboda ingancinsu, kuma sun samar da mafita ga sha’anin sufuri mai tsafta a farashi mai rahusa. (Yahaya)