CDC Afirka: Wadanda suka harbu da kyandar biri a Afirka sun kai kusan 30,000
2024-09-21 17:12:03 CMG Hausa
Cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta Afirka wato Afirka CDC ta ce, adadin wadanda ake tunanin sun kamu da cutar kyandar biri a Afirka ya karu zuwa 29,152, daga ciki wadanda aka tabbatar sun kamu sun kai 6,105 tare da mutuwar mutane 738, tun daga farkon wannan shekara ta 2024.
Da yammacin ranar Alhamis ne darakta janar na Afirka CDC Jean Kaseya ya tabbatar da hakan a yayin taron manema labaru da aka gudanar ta intanet, game da barkewar cutar kyandar biri a Afirka, inda ya ce, an samu rahoton masu kamuwa da cutar guda 2,912 a cikin makon da ya gabata kadai a nahiyar, daga ciki an tabbatar da kamuwar 374 sannan 14 sun mutu.
A baya-bayan nan dai, hukumar ta Afirka CDC ta sanar da kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya wato WHO don mayar da martani a nahiyar Afirka. Shirin na watanni shida, wanda za a gudana daga watan Satumban shekarar 2024 zuwa na Fabrairun shekarar 2025, yana da kiyasin kasafin kudi na kusan dalar Amurka miliyan 600. Daga ciki an ware kashi 55 cikin dari ga kokarin dakile cutar kyandar biri a cikin kasashen da abin ya shafa, yayin da sauran kashi 45 cikin dari aka karkata zuwa ga tallafi na aiki da fasaha daga kungiyoyin abokan hulda. (Yahaya)