logo

HAUSA

Xi ya jaddada ba da cikakkiyar dama ga fa'idar siyasa ta CPPCC

2024-09-20 20:10:03 CMG Hausa

Shugaba Xi Jinping ya yi kira da a kara ba da cikakkiyar dama ga babbar fa'idar siyasa ta majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC a fannin raya tsarin dimokuradiyyar jama'a baki daya.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar Sin, ya yi kiran ne a yayin taron murnar cika shekaru 75 da kafuwar CPPCC a nan birnin Beijing.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya kara da cewa, abubuwan da suka faru cikin shekaru 75 da suka gabata sun tabbatar da cewa, CPPCC wani sabon tsarin siyasa ne wanda ya kunshi jam’iyyun siyasa, da fitattun mutane wadanda ba su cikin kowace jam’iyya, da kungiyoyin jama’a, da jama’a daga bangarori daban daban, da dukkan kabilu a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. (Yahaya)