logo

HAUSA

Kwamitin da shugaban Najeriya kan aiwatar da sauye sauye a bangaren sha’anin kiwon dabbobi ya mika rahotonsa

2024-09-20 10:29:39 CMG Hausa

Kwamitin da shugaban tarayyar Najeriya ya kafa a kan aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi sha’anin kiwon dabbobi a kasar ya mika rahotonsa.

A jiya Alhamis 19 ga wata shugaban kwamitin Farfesa Attahiru Jega ya gabatar da rahoton ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa dake birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

An dai kafa kwamitin ne a watan Julin wannan shekara da nufin lalubo hanyoyin magance matsalolin dake kawo cikas ga zaman lafiyar manoma da makiyaya a kasar, tare kuma da bullo da sabbin tsare-tsaren zamani da zai amfanar da manoman da makiyayan da ’yan kasuwa da suke sarrafa madara da naman shanu.

A lokacin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan da mika rahoton, shugaban kwamitin ya ce, kwamitin nasu ya zakulo wasu matakai da gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da su cikin adalci da daidaito a kan yadda za a rinka cin gajiyar alheran dake tattare da kiwon dabbobi a kasar.

Farfesa Attahiru Jega haka kuma ya ce, kundin rahoton dai mai shafuka 152 ya baiwa gwamnati shawarwari da za ta yi amfani da su wajen kawo karshen rigingimun manoma da makiyaya a duk fadin Najeriya.

Ha’ila yau kuma kwamitin ya bayar da shawarar cewa, bai kamata lokaci guda a yi gaggawar dakatar da makiyaya daga ci gaba da bin tsarin kiwo na gargajiya ba, inda ya ce, akwai bukatar a baiwa makiyaya damar gwamutsa tsarin kiwon gargajiya da na zamani har zuwa lokacin da aka sami damar wayar da kan jama’a sosai da kuma samar da dukkannin kayayyakin da ake bukata a makiyayar zamani da gwamnati za ta samar.

A karshen rahoton, kwamitin ya bayar da hanyoyin da za a bi wajen gudanuwar ayyuka a sabuwar ma’aikatar lura da harkokin kiwo wanda shugaban kasa ya kirkira a kwanakin baya. (Garba Abdullahi Bagwai)