Wani jirgin sama na dakon kaya samfurin Y-20 na kasar Sin ya isa Pretoria
2024-09-20 13:58:42 CGTN Hausa
A ranar 18 ga watan nan, wani jirgin sama na dakon kaya samfurin Y-20 na kasar Sin ya isa wajen baje kolin kayayyakin sararin sama, da na tsaron kasa na Afirka da yake gudana a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu. Wannan ne karo na farko da irin wannan jirgin saman dakon kaya samfurin Y-20 na kasar Sin ya isa kasar Afirka ta kudu, tare da yin nune-nune a tsaye da ma motsi a bikin baje kolin. (Sanusi Chen)