logo

HAUSA

Amurka ta shirya makudan kudade don inganta matakan bata sunan kasar Sin

2024-09-20 21:48:33 CMG Hausa

Kwanan baya, majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da daftarin doka dangane da ware dalar Amurka biliyan 1.6 baki daya daga shekarar 2023 zuwa ta 2027 don tinkarar abin da suke kira “munanan illolin da kasar Sin za ta haddasa”. Sabon mataki na yin amfani da dalar Amurka wajen yin magudi tsakanin al’umma da kuma bata sunan kasar Sin ya tabbatar da cewa, Amurka, ita ce wadda ta yada labaran karya, lamarin da ke haifar da illoli kan huldar da ke tsakanin kasa da kasa da kuma akasarin ra’ayoyin jama’ar kasa da kasa.

A cikin wannan daftarin dokar, baya ga kalaman da Amurka ta sha ambato dangane da tsarin kasar Sin, Amurka ta bayyana cewa, an illata tsaron Amurka da tattalin arzikinta, da kuma tsarin kasa da kasa. Kana Amurka ta bata sunan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ta hanyar barin daidaikun mutane da rukunonin da gwamnatin Amurka ta mara musu baya ta fuskar kudi, su kitsa labarai. Dalar Amurka biliyan 1.6, adadi ne ya ninka kudin da CNN ta kashe wajen tafiyar da harkokinta a shekara guda har sau biyu. Kana kuma adadi ne ninka yawan kasafin kudin hukumar kafofin yada labaru na kasa da kasa ta Amurka har sau biyu. Masharhanta sun yi nuni da cewa, adadin ya nuna yadda matukar damuwar da Amurka ke nunawa, da kuma iyakacin kokarin da wasu suke yi na neman samun fifikon siyasa ta hanyar batawa kasar Sin suna.

Duk da haka shafa wa kasar Sin kashin kaji da dakile ci gaban kasar Sin ba za su warware matsalolin Amurka ba, kana ba za su hana ci gaban kasar Sin ba. Za su yi wa huldar da ke tsakanin Sin da Amurka zagon kasa, da illata moriyar kasar Amurka da Amurkawa, da kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Ya fi kyau ‘yan siyasan Amurka su tambayi kansu ko ya dace su kashe wadannan makudan kudade ba gaira ba dalili? (Tasallah Yuan)