Sin da Japan sun cimma matsaya daya kan zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku
2024-09-20 17:05:59 CMG Hausa
A ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2023, gwamnatin Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya na tashar samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya ta Fukushima cikin teku, bisa radin kansa. A matsayin daya daga cikin kasashen da abin ya fi shafa, Sin ta tsaya tsayin daka kan adawa da wannan aiki maras dacewa. Kwanan nan, manyan hukumomin da abin ya shafa na kasashen biyu sun tattauna da juna sau da dama, kan matsalar, kuma a karshe, sun cimma matsaya daya.
Bangaren Japan ya tabbatar cewa, zai sauke nauyin da ya rataya a wuyansa bisa dokokin kasa da kasa, zai yi iyakacin kokarin gudun haddasa mummunan tasiri ga lafiyar mutane da muhallin halittu, kuma zai ci gaba da gudanar da binciken tasirin aikin kan muhallin halittu na teku. A sa’i daya kuma, bisa damuwar dukkan kasashen da abin ya shafa kamar Sin, bangaren Japan yana maraba da kafa tsarin sa ido cikin dogon lokaci, a karkashin tsarin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA, kuma ya tabbatar da cewa, kasashen da abin ya shafa kamar Sin suna iya shiga ciki, kuma suna iya aiwatar da ayyukan neman samfur da kansu don dubawa da yin kiyasi a dakin gwaje-gwaje da sauransu. (Safiyah Ma)