An gudanar taro mai taken "A rubuce a Sama: Labarina na kasar Sin" don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a Riyadh
2024-09-20 21:37:01 CMG Hausa
A ranar 19 ga watan Satumba, an yi nasarar gudanar da taro mai taken "A rubuce a Sama: Labarina na kasar Sin", don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Shen Haixiong, babban darektan rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya bayyana a cikin wani jawabi ta kafar bidiyo cewa, a cikin jerin labaran da aka tattara a duniya, abokai daga kasashe fiye da 60 sun ba da labarin soyayya tsakanin Sin da kasashen waje fiye da 1,600. Haruffa daban daban sun isar da bayanan soyayya na bai daya, wadanda ke wakiltar hadewar soyayya mai zurfi da al'adun kasashen duniya, kuma suna dauke da burin jama'ar kasa da kasa kan zaman lafiya da kyawu, suna kunshe da matukar karfi na abokantaka tsakanin mutane, wanda ya zarce iyakoki da lokaci. (Yahaya)