An rubuta ra’ayin “kwayar zarra ta atom ta kawo alheri ga kasashe masu tasowa” na Sin a cikin kudurin hukumar IAEA
2024-09-20 11:36:23 CMG Hausa
An zartas da kudurin “karfafa ayyukan hadin gwiwar fasahohi na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA”, wanda kungiyar G77 da Sin suka mika tare, a babban taron IAEA karo na 68.
Karo na farko ne an rubuta ra’ayin “kasashen dake kudancin duniyarmu” a cikin kudurin, inda aka jadadda muhimmancin goyon bayan sashen sakatariyar hukumar wajen karfafa hadin gwiwa a fannin fasaha tsakanin kasashe mambobin hukumar, sannan aka yi kira ga kasashe masu sukuni da su samar da karin albarkatu ga kasashe masu tasowa don tallafawa hadin gwiwar fasahohi, da karfafawa kasashe masu tasowa gwiwar amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, ta yadda za a hanzarta cimma burin ci gaba mai dorewa.
Zaunannen wakilin Sin a IAEA, Li Song ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, yayin da ake tattaunawa kan kudurin, kasar Sin ta ba da shawarar manufar “kwayar zarra ta atom ta kawo alheri ga kasashe masu tasowa” , wanda kasashe masu tasowa suka yi maraba da su gaba daya. “Kwayar zarra ta atom ta kawo alheri ga kasashen dake kudancin duniyarmu” na da nufin bayyana bukatun gaggawa na kasashe masu tasowa a fannin amfani da makamashi da fasahohin nukiliya cikin lumana, tare da jaddada muhimmanci da kyakkyawar ma'anar kasashe mambobin hukumar su tallafawa ci gaban kasashe masu tasowa tare. (Safiyah Ma)