logo

HAUSA

An dage lokacin fara sabon zangon karatu a Nijer zuwa 28 ga Oktoba saboda ruwan sama

2024-09-20 09:57:13 CMG Hausa

Gwamnatin Nijer ta yanke shawarar dage lokacin fara sabon zangon karatu zuwa ranar 28 ga watan Oktoba, daga ranar 2 ga watan, saboda tsanantar yanayin a kasar. An yanke wannan shawara ne yayin taron majalisar ministocin kasar da ya gudana jiya Alhamis.

A cewar wata sanarwa da aka fitar, yayin shirye-shiryen zangon karatu na shekarar 2024-2025, an gano cewa, ambaliyar ruwa ta shafi makarantu da dama, yayin da sauran makarantun ke zaman mafaka ga wadanda suka rasa matsugunansu.

A cewar hukumar kare fararen hula dake birnin Niamey, mamakon ruwan sama da Nijer ta fuskanta tun da aka shiga yanayin damina a watan Mayu, ya yi sanadin mutuwar mutane 273 zuwa ranar 4 ga watan Satumba, inda wasu 710,767 suka rasa muhallansu.

Domin tunkarar wannan yanayi dake bukatar daukin gaggawa, zuwa ranar 17 ga watan Satumba, gwamnatin kasar ta raba sama da tan 9,742 na hatsi, da nufin taimakawa kimanin mutane 842,300 cikin iyalai kimanin 112,400 da ambaliyar ta shafa. (Fa’iza Mustapha)