logo

HAUSA

Kasar Sin sannu a hankali za ta dawo da shigo da kayayyakin ruwa na Japan

2024-09-20 19:48:35 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dawo da shigo da kayayyakin ruwa na kasar Japan ne kawai bisa shaidar kimiyya da sakamakon ayyukan sa ido. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta jaddada cewa, yayin da aka cimma yarjejeniya da kasar Japan, ba za a dawo da shigo da kayayyakin ruwa na Japan nan take ba. Kasar Sin za ta bi dokokinta da ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, da tabbatar da ingancin kayayyakin ruwa da ta shigo daga kasashen waje. (Yahaya)