logo

HAUSA

Sin da EU sun yi tattaunawa mai zurfi don gane da takkadamar haraji kan motoci masu aiki da lantarki

2024-09-20 10:29:30 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta ce bangaren kasar da Tarayyar Turai, sun yi tattaunawa mai zurfi da ma’ana, game da binciken dake gudana kan tallafin motoci masu aiki da lantarki na kasar Sin.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar jiya Alhamis, ta ce yayin tattaunawar tsakanin ministan kula da harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Wentao da mataimakin shugaban hukumar EU kuma kwamishinan kula da cinikayya na kungiyar Valdis Dombrovski, dukkan bangarorin biyu sun bayyana kudurinsu na warware sabanin dake akwai ta hanyar tattaunawa.

Har ila yau, sun amince da ci gaba da tattaunawa kan batun farashi, kuma za su ci gaba da kokari ba tare da kasa a gwiwa ba, domin cimma mafitar da za ta karbu ga kowa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna. (Fa’iza Mustapha)