An gudanar da bikin “A rubuce a Sama: Labarina na kasar Sin” don murnar cika 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a Abuja
2024-09-20 21:22:07 CMG Hausa
A ranar 17 ga watan Satumba, agogon Najeriya, an gudanar da taro mai taken “A rubuce a Sama: Labarina na kasar Sin”, wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko CMG ya shirya a Abuja domin murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.
Jakadan kasar Sin a Najeriya Yu Dunhai ya bayyana cewa, an samu labaru da dama masu burgewa, wadanda ke ba da shaidar dankon zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka. Kasashen Sin da Najeriya na da dadadden tarihin yin mu'amala. Tun bayan kulla huldar diflomasiyya fiye da rabin karni da ya gabata, dangantakar kasashen biyu ta jure sauye-sauye a kasa da kasa da kuma kara karfi. A taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024 na birnin Beijing, shugabannin kasashen biyu sun yanke shawarar daukaka dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa huldar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Sin da Najeriya za su yi aiki tare don ciyar da aikin zamanintar da kasa gaba, da ba da gudummawa sosai wajen kyautata jin dadin jama'ar Sin da Afirka, da kiyaye zaman lafiya da wadata a duniya. (Yahaya)