UNGA ya yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen mamayar yankunan Falasdinawa cikin wa’adin watanni 12
2024-09-19 11:08:29 CMG Hausa
Babban taron MDD ko UNGA, ya amince da wani kuduri dake kira ga Isra’ila, da ta kawo karshen mamayar da take yiwa yankunan Falasdinawa cikin watanni 12 masu zuwa.
Kudurin wanda aka zartas a jiya Laraba, yayin taron gaggawa na UNGA karo na 10 da rinjayen kuri’u 124, da kuri’un adawa 14, da kuri’u 43 daga kasashen da suka kauracewa bayyana matsaya, ya karkata ne ga bukatar dakile ayyukan da Isra’ila ke gudanarwa a gabashin birnin Kudus, da sauran sassan Falasdinawa da Isra’ila ta yiwa kaka-gida.
Bangaren Falasdinawa ne dai ya gabatar da kudurin a ranar Talata, da hadin gwiwar wasu karin kasashen sama da 20, wanda kuma ya bukaci Isra’ila ta yi biyayya ga dukkanin ka’idojin dake wuyan ta karkashin dokokin kasa da kasa, ciki har da ra’ayoyin shawarwari na kotun kasa da kasa. (Saminu Alhassan)