logo

HAUSA

Sin na fatan za a aiwatar da sabon daftarin da aka zartas kan batun Palesdinu da Isra’ila a taron musamman na babban taron MDD

2024-09-19 20:43:57 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, an zartas da daftarin kuduri kan batun yankunan Palesdinu da Isra’ila ta mamaye a gun taron musamman kuma na gagggawa na babban taron MDD a ranar 18 ga wannan wata, kasar Sin tana maraba da nuna yabo ga zartas da daftarin. Kana ta nuna goyon baya ga daftarin, da kada kuri’ar goyon baya, tana fatan za a gaggauta aiwatar da daftarin a dukkan fannoni. (Zainab Zhang)