logo

HAUSA

An gabatar da Y-20 a bikin baje kolin sararin samaniya da tsaro na Afirka

2024-09-19 12:53:38 CMG Hausa

An kaddamar da wani jirgin yaki na rundunar sojin saman kasar Sin samfurin Y-20, a bikin baje kolin sararin samaniya da tsaro na Afirka da aka bude a birnin Pretoria, babban birnin kasar Afirka ta Kudu, a jiya Laraba ranar 18 ga wata. Wannan ne karo na farko da Y-20 ya isa Afirka ta kudu, tare da yin nune-nune a tsaye da ma motsi a bikin baje kolin.

A yayin bikin, Y-20 zai kammala fasahohin sarrafa jirgi 5 a cikin mintuna kusan 10.

A ranar bikin bude taron, an jera jiragen yakin Y-20, da dimbin jiragen yaki daga kasashe daban-daban yadda ya kamata a wurin baje kolin, inda Sinawa dake Afirka ta kudu suka garzaya zuwa wurin don daukar hoto tare da wannan jirgi mai daraja da ma’ana daga kasar Sin.

A cikin ’yan shekarun baya-bayan nan, Y-20 na fita kasashen waje akai-akai don gudanar da ayyuka daban-daban. A shekarar 2022, an nuna jirgin a tsaye a bikin baje kolin sararin samaniya na Austria, tare da tashi zuwa Tonga don gudanar da aikin agaji na jin kai. A shekarar 2024, ya wuce ta kan Dalar Duwatsu tare da jirgin sama guda shida samfurin J-10 na kungiyar “August lst” ta rundunar sojan saman kasar Sin, kuma ya fara tashinsa na farko a ketare a filin jirgin sama na El Alamein a Masar. (Bilkisu Xin)