logo

HAUSA

Wang Yi zai halarci taron kolin MDD kan makoma da muhawara ta babban taron MDD karo na 79

2024-09-19 19:30:17 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya sanar a yau Alhamis cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi, zai halarci taron kolin MDD kan makoma, da muhawarar babban taron MDD karo na 79 a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, daga ranar 22 zuwa ta 28 ga watan Satumba.

Lin ya ce, a cikin wannan mako har ila yau, Wang zai halarci tarurrukan da kasar Sin za ta shirya, da suka hada da taron sa kaimi ga shirin ci gaban duniya, da na inganta hadin gwiwar kasa da kasa kan kirkirarriyar basira ko AI, da kuma tarurrukan bangarori daban daban da suka hada da babbar muhawarar kwamitin sulhu na MDD, da taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS, da na ministocin harkokin wajen kasashen G20. 

Kakakin ya kara da cewa, Wang zai gana da sakatare janar na MDD, da shugaban babban taron MDD karo na 79, da ministocin harkokin waje ko shugabannin kungiyoyin wakila na kasashen da abin ya shafa. (Yahaya)