logo

HAUSA

Bankin raya kasashen Afrika ya gamsu da sauye-sauyen tattalin arzikin da ake kan gudanarwa a Najeriya

2024-09-19 10:04:46 CMG Hausa

Bankin raya kasashen Afrika ya yabawa shugaban tarayyar Najeriya bisa yadda yake gudanar da sauye-sauyen tattalin arziki a kasar, inda ya bukaci da ya kara jajircewa ta fuskar wadata kasa da abinci.

Darakta janaral na bankin a Najeriya Mr. Abdul Kamara ne ya yi yabon ranar Laraba 18 ga wata lokacin da ya jagoranci ayarin jami’an bankin zuwa ofsihin ministan kudi na tarayyar Najeriya Mr. Wale Edun.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Tun da farko dai sai da Mr Abdul Kamara ya isar da sakon jajensa a madadin shugaban bankin na raya kasashen Afrika ga gwamnati da kuma al’ummar Najeriya baki daya bisa iftila’in ambaliyar ruwan da ya faru a birnin Maiduguri, inda ya tabbatar da cewa, a shirye bankin yake ya bayar da dukkan taimakon da ya kamata wajen dakile matsalolin da za su biyo bayan ambaliyar.

Ya ce dai, sun kawo wannan ziyara ce domin duba wasu bangarori na tattalin arziki da bankin zai taimakawa Najeriya, sannan kuma ya kara ankarar da gwamnati muhimmancin samu hada kai na kasa da kasa wajen dorewar ci gaba.

Wakili na bankin na AFDB a Najeriya ya shaidawa ministan cewa jinjinar da bankin ya yi wa shugaba Bola Tinubu ta fuskar sauye-sauyen tattalin arziki, wata alama ce dake nuna cewa Najeriya ta hau bisa turbar daidaituwar tattalin arziki da bunkasuwa, inda ya sake nanata aniyar bankin na taimakawa Najeriya domin ta shawo kan kalubalen karancin abinci a kasa.

Da yake jawabi, ministan kudi na tarayyar Najeriya Mr. Wale Edun ya yaba bisa wannan ziyara wadda ta bayar da damar tattaunawa a kan batun karfafa samar da abinci, gina cibiya ta musamman da za ta rinka sarrafa kayan amfanin gona, kana kuma an tabo sauran batutuwa da za su taimakawa bunkasar tattalin arzikin Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)