Kasar Sin na adawa da duk wani nau’in ta’addanci
2024-09-19 19:38:58 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a taron manema labarai da aka yi a yau Alhamis cewa, kasar Sin na jajantawa wadanda harin ta’addanci da aka kai a kasar Mali ya rutsa da su, tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa da wadanda suka jikkata.
An ba da rahoton cewa, a ranar 17 ga watan Satumba ne aka kai hare-haren ta’addanci da dama a Bamako, babban birnin kasar Mali, wanda ya haddasa hasarar rayuka da dama. (Yahaya)