Shugaban babbar hukumar kare bayanan sirri ta kasa ya yi rantsuwar kama aiki
2024-09-19 10:24:35 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, a ranar jiya Laraba ne 18 ga watan Satumban shekarar 2024, aka yi bikin rantsar da sabon shugaban babban hukumar da ke kula da kare bayanan sirri ta kasa dake birnin Yamai a gaban idon mambobin gwamnati da na kwamitin ceton kasa na CNSP, da kuma alkalan kotun kasa.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Shi dai shugaban babban hukumar kare bayanan sirri ta kasa HAPDP, Iro Adamou ya yi rantuwar kama aiki a gaban alkalan kotun kasa ko Cour d’Etat da Faransanci da cibiyar take birnin Yamai. Haka kuma a gaban idon jama’a ne, sabon shugaban hukumar ya dauki alkawalin yi wa kasa bauta, da yin aiki bisa adalci, da kuma kare muradun kasar Nijar bisa ayyukan dake gabansa. Kamar yadda dokokin kasa suka bayyana, sabon shugaban hukumar, da bai jima da aka nada shi mamba kuma daga bisani shugaban hukumar bisa kuduri mai lamba 4016/P/CNSP na ranar 24 ga watan Junin shekarar 2024 aka aza shi bisa aikinsa.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar