logo

HAUSA

Sin ta harba tagwayen taurarin dan adam na tsarin BeiDou

2024-09-19 14:59:26 CMG Hausa

A yau Alhamis kasar Sin ta yi nasarar harba tagwayen taurarin dan adam na tsarin hidimar taswira ta BeiDou-3 ko (BDS-3), daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar.

An harba taurarin biyu na 59 da 60 ne da karfe 9:14 na safiya bisa agogon birnin Beijing, ta amfani da rokar Long March-3B, da na’urar Yuanzheng-1 (Expedition-1) dake makale jikin rokar.

Wannan ne karo na 535 da aka yi amfani da roka samfurin Long March, wajen harba jerin taurarin bil adama na kasar Sin. (Saminu Alhassan)