Karuwar yawan al’umma na iya ingiza matsalolin sauyin yanayi a Afirka
2024-09-19 10:49:16 CMG Hausa
Sakamakon wani binciken kwararru ya nuna cewa, karuwar yawan al’umma na iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arziki da muhallin halittu, da yanayin ingancin rayuwar jama’ar sassan nahiyar Afirka.
Binciken wanda cibiyar nazari game da manufofin samar da ci gaba ta Afirka ko AFIDEP ta fitar a jiya Laraba, ya nuna cewa, daidaita adadin yawan jama’ar Afirka, na iya zama jigon shawo kan tasirin sauyin yanayi, da gurbatar muhalli, da lalacewar yanayin rayuwar mabanbantan halittu.
Kaza lika, binciken ya ce a wannan gaba da yawan jama’ar yankin kudu da hamadar Saharar Afirka ke karuwa duk shekara da kusan kaso 2.5, yankin na fuskantar barazanar tsunduma cikin mummunan tasirin sauyin yanayi, duk da cewa hayaki mai dumama yanayi da yankin ke fitarwa bai wuce kaso 3 bisa dari cikin jimillar wanda ake fitarwa a duniya baki daya ba.
Kwararru daga cibiyar AFIDEP sun ce ya zuwa shekarar 2100, kasashe 5 cikin 10 mafiya yawan al’umma a duniya za su kasance a nahiyar Afirka, yayin da bunkasar harkokin raya tattalin arziki, da sauyi a fannin bukatar amfani da filaye, da karuwar bukatar makamashi da sauran albarkatu, ka iya fadada fitar da iskar carbon mai dumama yanayi. (Saminu Alhassan)