An yi murnar bikin Zhongqiu a birnin Luzhou
2024-09-18 21:28:22 CMG Hausa
A ranar 17 ga watan Satumban 2024, an gudanar da taro mai jigon “mutane 10,000 da suka rera wakoki don murnar bikin tsakiyar kaka na Zhongqiu” a birnin Luzhou na lardin Sichuan.
mazauna wurin da masu yawon bude ido sama da 20,000 suka hallara a fagen bikin, kuma ya janyo kusan masu kallo ta yanar gizo 200,000. Ta hanyar wake-wake da raye-raye, da karatun wakokin adabi da sauran nau'o'in wasanni, nune-nunen da aka gabatar sun baiwa jama'a damar samun nishadi da jin dadin bikin na gargajiya, har ma sun kara fahimtar kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin.
A yayin bikin na Zhongqiu, birnin Luzhou ya samu masu yawon bude ido miliyan 1.85, kuma baki daya yawan kudin shiga da aka samu daga yawon bude ido ya kai yuan miliyan 350.